1 Corinthians 2

1Lokacin da na zo wurin ku, yan’uwa, ban zo da gwanintar magana ko hikima ba yayinda na yi shelar boyayyun bayanai game da Allah [ a yayinda na bada shaida game da Allah]. 2Domin na kudura a zuciyata kada in san komai lokacin da nake tare da ku, sai dai Yesu Almasihu, gicciyayye.

3Ina tare da ku cikin kasawa, da tsoro, da fargaba mai yawa. 4Kuma sakona da shelata basu tare da kalmomin hikima masu daukar hankali. Maimakon haka, sun zo da bayyanuwar Ruhu da iko, 5saboda kada bangaskiyarku ta zama cikin hikimar mutane, amma cikin ikon Allah.

6Yanzu muna maganar hikima ga wadanda suka ginu, amma ba hikima ta duniyan nan ba, ko ta masu mulkin wannan zamani, wadanda suke shudewa. 7Maimakon haka, muna maganar hikimar Allah ta boyayyar gaskiya, boyayyar hikima da Allah ya kaddara kafin zamanin daukakarmu.

8Babu wani mai mulki na zamanin nan da ya san wannan hikimar, domin inda sun gane ta a wancan lokacin, da basu gicciye Ubangijin daukaka ba. 9Amma kamar yadda yake a rubuce, “Abubuwan da babu idon da ya gani, babu kunnen da ya ji, babu zuciyar da ta yi tsammanin sa, abubuwan da Allah ya shirya wa wadanda suke kaunarsa.

10Wadannan ne abubuwan da Allah ya bayyana mana ta wurin Ruhu. Gama Ruhu yana bincika komai, har ma abubuwa masu zurfi na Allah. 11Gama wanene ya san tunanin mutum, sai dai ko ruhun mutumin da ke cikinsa? Haka ma, babu wanda ya san abubuwa masu zurfi na Allah sai dai Ruhun Allah.

12Ba mu karbi ruhu na duniya ba, amma Ruhun da ya zo daga wurin Allah, domin mu san abubuwan da aka bamu a sake daga wurin Allah. 13Muna maganar wadannan abubuwa da kalmomin da hikimar da mutum baza ta iya koyarwa ba, amma wadanda Ruhu ke koyar da mu. Ruhu yana fassara kalmomi na ruhaniya da hikima ta ruhaniya.

14Mutum marar ruhaniya ba ya karbar abubuwan da suke daga Ruhun Allah, gama wauta suke a gareshi. Ba zai iya sanin su ba domin Ruhu ne yake bayyana su. 15Shi wanda yake mai ruhaniya yana shari’anta dukan abubuwa, amma shi baya karkashin shari’ar sauran mutane. “Wa zai iya sanin zuciyar Ubangiji, da zai iya ba shi umarni?” Amma mu muna da lamiri irin na Almasihu.

16

Copyright information for HauULB